Wednesday, April 17, 2019

RAYUWAR `YAN MATA A JAMI`A

RAYUWAR `YAN MATA A JAMI`A
Dasunan Allah mai rahama mai jin ƙai, mamallakin sammai da ƙassai.
Inaso a cikin damar da Allah ubangiji ya bamu na mallakar wannan kafa mai Albarka nadan dangwali tawada domin tofa Albarkacin baki akan irin Rayuwa mai tarin sarƙaƙiya wato RAYUWAR `YAN MATA A JAMI`A .
Tabbas wannan Al`amari babba ne, kuma abin a tausayawa wadanda abin ya shafa ne, kuma tabbas idan har kana da kishi da tausayi koda gwargwadon kwayar zarra a cikin zuciyarka matukar kasan ire-iren abunda ke faruwa lallai zaka tausaya.
Mace a Jami`a tamkar Yankan nama ne a tsakanin kuraye a yayin da kowacce yunwa ta isheta, zaka iya yarda da maganata idan
kayi duba na basira ga rayuwar da suke gudanarwa acan, BA INA SUKAR KARATUN MACE BANE A JAMI`A ina kokarin naga na saka tausayinsu a zuciyar Al`ummah ne.
Mace kadai ce a jami`a zaka ga tana da kalubale ta kowane bangare. Ta bangaren dalibai `yan uwanta akwai course mate wanda mafi yawanci sunanan suna kyalla  ido suga wacece kyakkyawa su makale mata, ba batun soyayya ne ya kawo su gurinta ba, ba kuma Al`Amari na karatu ba, ba `yar uwar su ce ba, a a kawai saboda chilling ko flexing wato su kawai su jero da ita ace wancan ya cinye kawai abinda sukeso Kenan, wasu ko `yan bata tarbiyya ne kawai suga sun lalata yarinya ba don suma su Aureta ba za dai tasha karya ne kawai sudai kawai `yan soyayya dadine. Akwai `yan uwanta mata kuma musamman idan tana da kokari tabbas zata sha hassada daga garesu, abin dubawar anan shine itafa jami`a ba makaranta ce da za`a ce wane yaci na daya ko wane yaci na karshen aji bane ballantana ace ai saboda ta wuce watane ko kuma sunyi kankankan to amma bansan abinda ke kawo wannan hassadar ba, idan kuwa akai rashin sa`a ta kasance cikin wadanda basu da kokari tofa tabbas izgili da wulakanci su zasu dinga take mata baya. Babban abinda yafi komai muni kuma shine harin da `yan mata yan maƌigo suke kaiwa musmman wadanda suka ga cewa salihan bayi ne, wannan ƙazamar ƌabi`a ta yawaita musamman ga `yan mata masu zama a hostels( bance duka ba), ta inda zakaga mace na neman `yar uwarta mace iyazan billah wato lesbianism. Akwai kuma Musibar da tafi kowace ban tsoro
ita musibar Cultism wacce ta zama ruwan dare zagaye duniya, wanda wannan shine mafi girman kalubale ga daliban jami`a( matan da mazan) musamman `yan ajin farko, kodai sum aka tayi ka karba kokuma suyi maka barazanar mutuwa wanda ta dalilin hakan wasu da dama ke afkawa wannan sharri domin basa so su mutu ( saidai sun manta Allah shike kashewa da rayawa a duk lokacin daya so), sukanyi Al`bishir ga duk wanda ya karba cewa zasu inganta rayuwarsa ta hanyar sanyashi cin jarabawa koda bai yi  karatu ba kokuma suyi baerazanar hana ka cin jarabawar idan ka ki. Idan kuma mace ta samu ta tsallake wadancan matsaltsalu akwai wata gagaruma kuma wannan itace gurbatattun lecturers wadanda su kuma burinsu shine mace ta yarda ta basu hadin kai su kuma su bata maki koda kuwa bata cancanci wannan maki ba idan kuwa akai rashin sa`a taki amincewa da bukatarsu to zasu san duk yadda zasuyi suga sun kada ita koda kuwa tafi kowa kokari, babu ruwansu da ita din mai kamun kaice kokuma fitsararriya, `yar talaka ce ko kuma `yar mai kudi, musulma ce ko kafira sudai mace dai mace, rashin tsoron Allah kuwa ba`a Magana domin duk irin hadashi da Allah da zatayi shi ko ajikinsa ballantana ya saduda. A gida kuma iyaye na jira ne ta kawo musu good result wanda shima kalubale ne a gareta, ga Al`ummar unguwa wasu kallon yan jami`a kawai suke a matsayin yan tasha duk sanda aka ce wance `yar jami`ace to kallon mutunci kuwa raguwa yake a idon jam`a, ga uwa uba samari masu neman Aure ba kasafai suke Auren `yan jami`a ba muamman wadanda suma sukai jami`ar badon kome ba hujjar su kawai bata wuce tantamarsu akan anya ta tsallake wadancan matsaltsalu na sama? Bayansu akwai bata gari na cikin Al`ummah wadanda su kuma aikinsu shine shiga jami`a musamman da yammaci domin zabo `yan mata a tafi outing dasu, sannan kuma su dawo gida a zauna dasu anan zagin su `yan matan.
Duk wadancan matsaltsalu kuma akwai shedan shikuma a gefe yana nan yana dubawa duk wacce ta kauce wa laifi sai yasan yadda yayi ya saita ta ta tafi akan Alkawarin da yayi wa Allah sedai idan ta kasance daga cikin bayin Allah na kwarai.
Meye mafita?
Ni a ganina mafita bata wuce lizimtar roƙon ubangiji tare da dogewa kan koyarwar Annabin rahama (Annabi Muhammad ) bisa ga tafarkin magabata na kwarai.


Shawara ga `yan mata
Shawarar da zan iya ba `yan mata wadanda suke ciki da wajen Jami`a shine kuji tsoron Allah wanda ya halicceku, duk abinda kuka aikata a fili ko a boye to tabbas yana kallonku domin shi babu wani abu dake iya buya daga gareshi, kuma a ranar da kowace gaba zatayi Magana zai tambayeku akan abin da kuka kasance kuna aikatawa a rayuwarku ta duniya. Sannan ya kamata ku sani duk wata irin kima da mace keda shi to yana cikin hijabinta na mutunci a duk lokacin da wannan hijabi ya yaye to ita mace bata da wani sauran kima a idon kowaye koda kuwa shine wanda ya taimaka mata wajen cire wannan hijabin mutuncin, domin shi kallon out dated yake mata, don haka a matsayinki na mace ki kare mutuncinki da na gidanku shi yafi. Allah yasa mu dace.
Shawara ga iyaye
Kun fini sanin irin kuncin da kuke shiga idan kuka ga `ya`yanku sun lalace, domin kuwa sakamakon hakan kanku yake fara komawa, duk wani mai zargi bazai taba zargin `yar a matakin farko ba sai ya dangana da irin tarbiyyar da kuka bawa `yar ko da kuwa kunyi iya bakin kokarinku wajen ganin kun saita ta a kan tafarki madaidaici.
Shawarar da zan baku dai bata wuce sa ido da dogewa wajen tabbatar da `yarku tana da kawaye na gari, domin babu abu mai canza tarbiyyar mutum a lokaci guda irin Aboki, zaku iya ku dauki fiye da shekara goma sha takwas kuna gina ma `yarku matakalar takawa domin zuwa tudun mun tsira amma a cikin dakiku kadan sai kawa mara tsoron Allah ta rusheshi. Zabarwa `ya`ya uwa ta gari da uba nagari  yana matukar taka rawar gani wajen taimakawa `yarku ta zamto ta kirki.
Babban ginshiƙi kokuma ince gadon baya shine Addu`a, domin kwarai da gaske Al`amarin Tarbiyya saida Addu`a.
Abin lura
Duk  wadancan Abubuwanda na lissafo wadansu na gani da idona wadansu kuw naji labari daga majiya mai karfi, dukda cewa har yanzu ban gama sanin sauran matsaltsalun ba. Wadansu kalmomin danai Amfani dasu kuwa na jami`ar ne sakamakon zama da ma`a bota su.
Bana nufin kowace jami`a haka take amma tabbas mafi yawanci suna tattare da wadannan abubuwa masu matukar rikitarwa. Mai karatu kaima nasan zaka iya sanin wadan su matsalolin ba wadannan ba , idan kuma kanada shawara zaka iya comment da taka shawarar mudai fatanmu shine a gyara.
Muna fatan Allah ya shiryar damu da kuma zuriyarmu baki daya .
Da wannan ni AHMAD ABDULKAREEM AL-ABSHATY nake cewa:
الزرع إن طاب يُحصد ذاك قيمته** والكفّ في ذا طبيب فاته العقل

No comments:

Post a Comment

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...